ABNA24 : Shugaba Rouhani ya bayyana hakan ne a wani taro da yayi da ‘yan kwamitin faɗa da cutar ta COVID-19 na Iran a jiya Asabar din ya ce: Ana ta ƙoƙari wajen ganin an fara amfani da rigakafin COVID-19 ɗin a cikin wannan wata na Bahman, lalle wannan babban aiki ne.
Shugaba Rouhani ya ce a sabuwar shekara ta watan farisanci da za ta fara a ranar 21 ga watan Maris, za a samu wasu rigakafi guda uku da Iran ta samar da su.
A watan da ya kama ne dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ɗin ta ƙaddama da shirin gwajin rigakafin nata a jikin ɗan’adam bayan ta kammala dukkanin abubuwan da ake buƙata da kuma samun dukkanin umurnin da take buƙata.
Iran dai ta sanar da aniyarta na sayen wasu rigakafin daga wasu ƙasashen da take da tabbaci kan kayayyakinsu kafin ta samar da nata ɗin don tabbatar da lafiyar ‘yan ƙasar, sai dai kuma ta sanar da cewa ba za ta sayi rigakafin da aka samar daga kamfonin Amurka da Birtaniyya ba bayan haramcin hakan da Jagoran juyin juya halin Musuluncin na ƙasar, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sanar saboda rashin tabbas ɗin da suke da shi.
342/